Putin ya goyi bayan takarar al-Sisi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sisi alheri ne; in ji Putin

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya yi wa shugaban sojin Egypt, Abdul Fattah al-Sisi fatan alheri a takarar shugaban kasar da ake sa ran zai yi.

Mr Putin ya bayyana hakan ne lokacin da su ke fara tattaunawa a bayan garin Moscow.

Ya ce takarar al-Sisi alheri ne ga Egypt.

Kawo yanzu dai Field Marshal al-Sisi bai kaddamar da takarar ba duk da dakarun sojin Egypt sun bukace shi da ya fito.

A lokacin tattaunawar ta su da shugaban Rasha ana sa ran za su rattaba hannu kan wata yarjejeniyar cinikin makamai.