Boko Haram: Ana bukatar karin dakaru a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mazauna Maiduguri sun ce a wasu lokuta 'yan Boko Haram sun fi sojoji manyan makamai

Gwamnan Jihar Borno a arewa maso gabacin Najeriya ya bukaci da a tura karin dakaru domin yaki da 'yan gwanwarmayar Boko Haram.

Kashim Shettima na magana ne a lokacin da ya ziyarci garin Konduga a inda mutane kusan 40 sun mutu a sakamakon wani hari a ranar talata.

Ya ce sojin Najeriya da 'Yan sanda na iya kokarinsu, to amma 'yan Boko Haram sun fi su makamai masu inganci.

Shettima ya ce " A gaskiya jami'an rundunar sojin Najeriya da 'yan sandan Najeriya na yin iya kokarinsu a irin halin da ake ciki. To amma kai da ni mun san cewar yan Boko Haram suna da makaman da suka fi inganci da kuma kuduri. Amma akwai bukatar karin dakaru da kuma karin goyon baya ga soji".

Shedu dai sun ce 'yan bindigar da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun isa garin da motoci da yawa,suka kafa wata bakar tuta a tsakiyar garin kafin harbi da yanke wasu daga cikin mutanen da suka kashen da kuma cunna wa gine gine wuta.

Karin bayani