Soji na fama da karancin makamai a Borno

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sojoji na zubar da makamai su tsere a Borno.

Sanata mai wakiltar Borno ta tsakiya a majalisar dattawan Nigeria, Ahmed Zannah ya koka da karancin kayan aikin da sojoji ke fama da shi a yankin arewa maso gabashin kasar.

Sanata Zannah ya shaida wa BBC cewa 'yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a yankin ne saboda karancin makamai da sojojin da ke yaki da su ke fama da su.

Ya ce kwamandojin soji a yankin sun tabbatar ma sa basu da wadatattun kayan aiki kuma sun koka zuwa ga gwamnatin tarayya amma tsawon watanni biyar ko bindiga guda ba a kara musu ba.

A cewar sanatan, hakan ce ta sa sojojin ke zubar da bindigoginsu su na tserewa idan aka kai hari, inda su kuma maharan ke kwashe wa su na kara karfi.

Wannan bayanin na zuwa ne bayan da maharan da ake jin 'yan Jama'atu Ahlis Sunnah lid Da'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ne su ka hallaka akalla mutane 40 tare da jikkata wasu da dama a garin Konduga da ke jihar Borno.

Karin bayani