Yaki ya kara rincabewa a sassan Syria

Rikici a kasar Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikici a kasar Syria

Masu fafutuka a Syria sun ba da rahoton karuwar fada a sassa dabam-dabam na kasar, wanda kuma ya fi muni a kan iyakarta da Lebanon.

Wata kungiya da ke sa ido kan keta hakkin dan adam a Syria ta ce ana kashe sama da mutane 200 a kullum tun fiye da makonni uku da su ka wuce.

Hakan na faruwa yayin da sojojin gwamnati da 'yan tawayen ke gwagwarmayar kwato karin wasu yankuna - mai yiwuwa da nufin karfafa matsayinsu a wurin sasantawa a tattaunawar neman sulhun dake gudana.

Wakilin BBC yace, a Yabroud na kan iyakar Syriya da Lebanon aka fi gwabza fadan a 'yan kwanakin nan, a yayin da sojojin Syria da 'yan Hizbollah dake maara musu baya ke kokarin kwace garin dake hannun 'yan tawaye.

Jami'an Rasha da Amurka za su shiga tattaunawar neman zaman lafiyar a Geneva ranar Alhamis inda bangarorin biyu suka dan samu 'yar fahimtar juna.