Thailand ta mayar da Musulmi 1300 Burma

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Musulmin Rohingya na tsere wa daga Burma a kwale-kwale.

Mahukuntan Thailand sun ce sun iza keyar Musulmi masu neman mafaka 'yan kabilar Rohingya 1,300 zuwa Burma.

An dai tsare mafi yawan Musulmin da su ka tserewa kasar tasu ne a wasu sansanonin Thailand kafin iza keyarsu zuwa gida.

A bara ne aka mayar da 'yan Rohingya zuwa gida amma sai yanzu labarin ya fito.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama dai sun yi tur da korar 'yan gudun hijirar,, inda su ka ce za su iya fuskantar matsi a kasar Burma, wacce yanzu ake kira Myanmar.

A baya bayan nan dai mabiya addinin Buddha masu rinjaye a Burma sun sha kai farmaki kan Musulmi 'yan kabilar Rohingya.