Ranar sauraren rediyo ta duniya

Wani Bafulatani makiyayi
Image caption Fulani makiyaya sun shaku da rediyo

Ranar sha uku ga watan Fabrairu, rana ce da hukumar UNESCO ta ware musamman, don kara fadakar da jama'a game da muhimmancin rediyo a fagen harkar yada labarai.

Manufar wannan rana ta bana, ita ce amfanin da jama'a ke samu daga sauraren rediyo da kokarin daukaka muryar mata, a kuma kara karfafa gudunmawar da suke bayarwa ta hanyar aiki a wannan kafa ta rediyo.

Rediyo, hanya ce mai sauki ta saduwa da jama'ar dake zaune a yankuna masu nisa, Fulani makiyaya na daga cikin al'ummomin da suka shaku da rediyo, kuma sun ce suna samun amfani mai yawa daga sauraren shirye-shiryen da ake watsawa a rediyo, kama daga labaran duniya zuwa rahotanni kan yadda za su kyautata sana'arsu ta kiwo.