Boko Haram: Mutane na tserewa daga Madagali

Image caption Akwai 'yan gudun hijirar Nigeria 40,000 da suka tsallaka Niger

Rahotanni daga jihar Adamawan Nigeria na cewa jama'a da dama na tserewa daga kauyukansu a cikin karamar hukumar Madagali, bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai kan jami'an tsaro, wanda ya yi sanadiyar kashe sojoji akalla tara.

Harin dai ya wakana ne a kauyen Izhe dake cikin karamar hukumar ta Madagli dake iyaka da jihar Borno da kuma Jamhuriyar Kamaru.

Rahotanni dai na cewa mutane da dama sun tsallaka zuwa Jamhuriyar Kamaru saboda zaman zullumin da suke ciki sakamakon rikicin dake da nasaba da 'yan Boko Haram.

An dai samu karuwar mutanen dake ficewa daga Nigeria dinne sakamakon kashe wasu sojoji tara da 'yan Boko Haram suka yi a Madagali.

Shugaban karamar hukumar ta Madagali, Maina Ularamu, wanda ya tabbar da kashe sojojin ya ce an kwashe gawarwakin sojojin zuwa babbar cibiyar kiwon lafiya ta Tarayya dake Yola babban birnin jihar ta Adamawa.

Jihar ta Adamawa dai na daya cikin jihohi uku na arewa maso gabashin Nigeria da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kafa wa dokar ta baci a watan Mayun bara da nufin yaki da masu tayar da kayar baya musamman 'yan Boko Haram.

Karin bayani