Kenya ta zargi Amurka da makarkashiya

Image caption Amurkan ta kara da cewa ita babbar kawar gwamnatin Kenyan ce

Amurka ta musanta zargin cewa ta mara baya ga zanga zangar kin jinin gwamnati da masu adawa suka yi a Kenya.

Kwamitin ba da shawarwari kan al'amuran da suka danganci tsaro na kasar Kenya ne ya zargi hukumar ba da agaji ta Amurka, USAID da kokarin hambarar da gwamnatin Kenyan ta hanyar tallafa wa masu adawa da gwamnatin.

A ranar Alhamis 'yan sanda sun yi amfani da hayaki me sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga zanga a babban birnin kasar, Nairobi.

Kwamitin ya ce yana da ingantattun takardun da ke nuna shedar cewa hukumar ta Amurka ta taimaka da kudade wajen shirya zanga zangar.

Sai dai kuma jakadan Amurka a Kenya Robert Godec ya musanta zargin.