'Babu batun juyin mulkin soji a Libya'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Zeidan na fuskantar matsin lamba saboda tabarbarewar tsaro a Libya

Firaministan Libya, Ali Zeidan ya yi watsi da jita-jitar cewar mai yiwuwa soji sun kwace mulki, yana mai cewar gwamnati na iko da dukan cibiyoyin gwamnati.

Mr Zeidan na mayar da martani ne a kan wata sanarwar da wani tsohon kwamandan soji yayi, wanda ya bukaci soji da su jagoranci kasar har ya zuwa wani sabon zabe.

Masu aiko da rahotanni sun ce tsohon hafsan sojin kasar , Janar Khalifa Haftar, ba yana magana ne da yawun hukuma a lokacin da ya yi kalamin a tashar TV ta Al-Arabiya mallakin Saudiya ba.

Babu dai wata alama ta zurga-zurgar soji a wajen muhimman gine-ginen gwamnati a Tripoli.

Karin bayani