Jam'iyyar MNSD ta kori jigoginta a Niger

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban jam'iyyar MNSD, Alhaji Seini Oumarou

Babbar jam'iyyar adawa a Jamhuriyar Nijar, MNSD ta kori jigoginta tara da su ka karbi mukaman ministoci a gwamnati, abinda ya saba wa matakin jam'iyyar na kin shiga gwamnatin .

Jami'an dai sun hada da sakataren jam'iyar Malam Albade Abuba, da Alhaji Alma Umaru daga jihar Damagaram, da Ada Shaifu daga jihar Tillabery.

Matakin ya biyo bayan wani taron gaggawa na ladabtarwa ne da kwamitin kolin jam'iyyar ya kira karkashin jagorancin shugaban jam'iyyar Alhaji Seyni Omar.

Sai dai wasu daga cikin mutanen da jam'iyyar ta kora sun ce hakan ya saba wa dokoki da ka'idojin jam'iyyar.