Amos ta nemi a hana yin kawanya a Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sama da mutane miliyan 9 na neman agaji a Syria

Babbar jami'ar ba da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos ta shaidawa kwamitin tsaro cewa ba daidai ba ne bangarori masu gaba da juna a Syria su ci gaba da saba dokokin ba da agaji na kasa da kasa.

Amos ta yi kira ga kwamitin tsaron da ya gabatar da kudirin da zai ba da damar shiga yankunan da aka yi wa kawanya sosai.

Ta ce bangarorin biyu a Syria sun gaza sauke nauyin da yake wuyansu na kare fararan hula.

Kawo yanzu dai an fitar da mutane 1,370 daga tsohon garin Homs; amma akwai mutane sama da 250,000 da har yanzu su na makale a garuruwan da aka yi wa kawanya a fadin kasar.

Karin bayani