Za a kawo karshen kiki-kaka kan Syria

Hakkin mallakar hoto c
Image caption Amurka da Rasha za su shiga tsakani a tattaunawa kan Syria

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya kan rikicin Syria Lakhdar Brahimi, wanda ke shiga tsakani a tattaunawar zaman lafiya a Geneva, ya ce manyan jami'an Amurka da na Rasha sun yi alkawarin yin duk abin da za su iya domin kawo karshen kiki-kakan tattaunawar.

Mataimakiyar Sakataren harkokin wajen Amurka Wendy Sherman da takwaranta na Rasha Gennadi Gatilov sun yi tattaki zuwa Genevan domin karfafa tattaunawar.

Tattaunawar kwanaki uku tsakanin gwamnatin Syria da tawagar 'yan adawa ta gaza cimma wata nasara ta a zo a gani.

Ana zargin gwamnatin Syria da masu adawa da ita da keta dokokin ba da agaji na kasa da kasa.

Karin bayani