Dakaru sun kwace makamai a Bangui

Hakkin mallakar hoto

Dakarun Faransa dana Tarayyar Afrika masu aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya sun kwace makamai daga mayakan sa-kai a Bangui, babban birnin kasar.

Dakarun sun yi awanni da dama suna bi gida-gida a wata unguwa a arewacin Banguin da aka yi imanin cewa mattarar Kiristoci ce dake kai hari akan Musulmai.

Cikin makaman da aka kwace harda bindigogi masu sarrafa kansu da kuma albarussai.

Faransan dai ta ce za ta tura karin dakaru 400 zuwa Jamhuriyar Afrika ta tsakiya domin kokarin kawo karshen tashin hankalin -- hakan zai kawo yawan sojojin Faransa a kasar zuwa 2,000.

Dakarun Faransan dai na aiki ne tare da dakaru 5,500 na kasashen Afrika.

Shugaba Francois Hollande na Faransan ya roki Majalisar Dinkin Duniya da tayi kokarin ganin cewa sojojin sun isa cikin hanzari.

Dubun dubatar Musulmi dai sun tsere daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar bayan da mayakan sa-kai Kiristoci suka cigaba da kai masu hari a cikin 'yan makonnin nan.

Mayakan sa-kan sun yi ikirarin cewa su na ramuwar gayya ne akan abinda Musulmi 'yan tawaye suka yi masu a bara.

Karin bayani