Za a binciki sojin Colombia

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban Colombia Juan Manuel Santos yace yaji mamakin zargin cin hanci da rashawa a rundunar sojin kasar.

Wata mujallar kasar ce ta wallafa zargin.

Mujallar mai suna Semana tace ta nadi hirarrakin da ke nuna cewa manyan hafsoshin sojin kasar na yin sama da fadi kudade da yawa.

Shugaban yace za a gudanar da cikakken bincike