'Yan gudun hijira sun kai dubbai a Diffa

Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption 'yan gudun hijirar Najeriya a Nijer na bukatar abinci

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa dubban 'yan gudun hijira ne da suka tsere daga hare-haren 'yan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya ke zaune a yankin Diffa na Jamhuriyyar Nijar.

A kwanan baya ne kuma jami'an hukumar da na gwamnatin Nijar suka kai ziyarar gani da ido a jihar ta Diffa, inda aka kiyasta cewa 'yan gudun hijirar kimanin dubu arba'in ne ke zaune a birnin.

Hukumar 'yan gudun hijirar dai ta sha alwashin tallafawa 'yan gudun hijirar da ke zaune a garuruwa fiye da dari na Nijar din.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar dai sun ce ba za su koma Najeriya ba saboda tashin hankula da suka fuskanta a kasar.

Yawancin su dai 'yan kauyukan da ke kusa da Diffa din ne a Najeriya wadanda ke arewacin Borno.

Karin bayani