An tashi baram-baram a taron sulhun Syria

Hakkin mallakar hoto Reuters

An kammala zagaye na biyu na taron sulhunta rikicin Syria batareda cimma matsaya ba.

Mai shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya Lakhdar Brahimi ya nemi afuwar jama'ar Syria akan yadda aka tashi baram baram.

Ya zargi tawagar gwamnatin Syria da kin amincewa da batutuwanda ya gabatar da suka hada da tattaunawa akan gwamnatin wucin gadi.

Bai tsaida rana ba akan lokacinda za a sake hawa teburin tattaunawa.

Karin bayani