An kai sabon hari a kudancin Borno

Hakkin mallakar hoto AP

An kashe mutane da dama a wani harin da 'yan bindiga suka sake kaiwa a Jihar Borno dake arewa-maso-gabacin Najeriya.

Rahotanni sun ce an kai harin ne a daren jiya a garin Izge dake Karamar Hukumar Gwoza dake kudancin jihar.

Mazauna garin sun ce wadanda su ka kai harin sun shiga garin ne dauke da bindigogi, suka yi ta harbin jama'a.

Sun kuma shiga har cikin gidaje suna kashe mutane, inji wadanda suka tsira.

Haka kuma 'yan bindigar sun fasa shaguna sun kwashi dukiyar jama'a kafin su fice daga garin.

Mutane da dama sun tsere daga garin zuwa wasu sassan Jihar Bornon da makwabciyarta Jihar Adamawa.

Wannan ne dai karo na biyu, cikin mako daya tak, da aka kai hari a garin na Izge. A harin makon jiya, 'yan bindiga sun kashe akalla sojoji tara.

Karin bayani