Moqtada al-Sadr ya bar Siyasa

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Malamin ya kuma ce ba zai tura wani wakilci majalisar kasar ba

Malamin nan na Shia maras sassauci a Iraqi, Moqtada al-Sadr, ya bayar da wata sanarwa ta ficewarsa daga harkokin siyasa.

A sanarwar da ya rubuta da hannunsa wadda ta zo da bazatta, da kuma aka sanya hoton takardar a shafinsa na intanet al-Sadr ya ce ba zai rike wani mukami na gwamnati ba.

A sanarwar ya kuma bayyana rufe dukkanin ofisoshinsa in ban da na ayyukan agaji.

Malamin da dakarunsa da ake kira sojojin Mahdi sun samu tasiri a Iraqi bayan sojojin Amurka sun yi wa kasar kutse a 2003.

Aamma kuma a 'yan shekarunnan ya rasa wannan tasiri sakamakon rashin jituwa da Fraiminista Nouri al-Maliki.

Karin bayani