CAR: An kubutar da musulmai 2,000

Hakkin mallakar hoto
Image caption An jibge dakarun kiyaye zaman lafiya a Bangui

Dakarun kasashen Afirka masu aikin kiyaye zaman lafiya sun samu sun kwashe Musulmi kimanin dubu biyu da ke tserewa daga jamhuriyar tsakiyar Afirka suna nufar Kamaru, sakamakon hare-haren da mayakan sa-kai na Kirista ke kai masu.

Wani wakilin BBC da ke tafiya tare da sojojin Rwanda ya ce, an kaiwa ayarin motocinsu hari da bindigogi da baka da kwari da takubba da duwatsu da kuma adduna.

Dakarun Rwandar sun maida martani a kan mayakan sa-kan da ke kokarin kashe duk wani dan gudun hijirar da suka samu.

An hallaka mutane goma da suka hada da Musulmi biyu 'yan gudun hijira, da kuma direban wata babbar mota.

Karin bayani