Izge: Dakarun Nigeria sun nuna fushinsu

Dakarun tsaron Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shelkwatar tsaron Najeriya ta ce ba gudu ba ja da baya wajen murkushe masu tada kayar baya a kasar.

Hedikwatar dakarun tsaron Najeriya ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kaiwa a wasu kauyukan jihar Borno wanda yayi sanadiyar asarar rayukar fararen hula da dama.

A wata sanarwa data fitar, hedkwatar tsaron ta kuma bukaci jama'ar yankunan da lamarin ya shafa da su gaggauta sanar da jami'an tsaro da zarar sun ga wani abu.

Inda ta jaddada cewa hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a 'yan kwanakin nan, ba zai sa guiwar su ta yi sanyi ba a kokarin da suke yi na magance ayyukan ta'addanci a kasar.

Shalkwatar ta ce a yanzu haka dakarunta sun zage dantse wajen farautar masu tada kayar baya da suka addabi jama'a a wasu yankuna na Jihar Maiduguri, da Yobe da kuma Adamawa kamar yadda Birgediya Janar Chris Olukolade ya fada a wata sanarwa da suka fitar.

Wannan abin takaici ne

Itama dai da take tsokaci game da hare-haren da aka kai a 'yan kwanakin nan kungiyar Jama'atu Nasrul Islam tace abin takaici ne duba da yadda ake kashe bayin Allah wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

Kungiyar tace kuma hakan na faruwa ne duk da irin tabbacin da hukumomi ke yi na magance wannan matsalar nan ba da jimawa ba.

Jama'atu Nasrul Islam ta nemi a kawo karshen wadannan hare- hare.

Karin bayani