Iran ta gargadi Pakistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Iran ta ja kunnen Pakistan akan masu gadin ta

Iran ta gargadi Pakistan cewa zata iya aikewa da dakaru cikin yankinta domin su kubutar da masu gadin kan iyakar Iram da aka sace idan har Islamabad bata dauki matakan sakin su ba.

Kalaman Ministan cikin gidan Iran na zuwa ne fiye da mako guda bayan da wata kungiyar 'yan bindiga tace ta yi garkuwa da masu gadi biyar a lardin Sistan-Baluchestan na kudu maso gabashin Iran

Kungiyar 'yan bindigar ta shata wasu sharudda da suka hada da sakin mambobinsu 50 kafin su sako masu gadin kan iyakar Iraniyawa