Ukraine ta yi afuwa ga masu zanga zanga

Hakkin mallakar hoto c
Image caption An shafe makwanni ana zanga zangar a Ukrain

Masu gabatar da kara a Ukrain sun ce a yau Litinin afuwar da aka shirya yi wa mutanen da aka tsare kan zanga zangar adawa da gwamnati za ta fara aiki.

Babban mai gabatar da kara na kasar ya ce masu zanga zangar sun cimma sharudan da aka gindaya na ficewa daga gine-ginen gwamnati da suka mamaye domin watsi da tuhumar da ake musu.

A ranar Juma'a gwamnatin ta sanar da sakin sama da mutane 232 da ta tsare.

Wakilin BBC a birnin kiev ya ce matakin alama ce ta sassaucin dambarwar da ke tsakanin bangarorin biyu, duk da cewa har yanzu ana cigaba da zanga zangar.