Zagayen farko na tattaunawar nukiliyar Iran

Tashar nukiliyar Iran Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tehran dai tun farko tace aikace aikacen nukiliyar ta na zaman lafiya ne

Iran tare da wasu Kasashe masu karfin fada aji su shida zasu soma zagayen farko na tattaunawa a yau game da wata yarjejeniya ta dogon zango da aka cimma akan shirin nukiliyar Iran mai cike da takaddama.

Za a gudanar da tattaunawar ne domin dorawa akan wata yarjejeniyar wucin gadi da aka cimma a watan Nuwamba bara.

Karkashin waccar yarjejeniyar Iran ta amince ta dakatar inganta makamashin uranium dinta idan har Kasasashen duniya suka sassauta mata takunkumin da aka kakaba mata.

Tehran dai tun farko tace aikace aikacen nukiliyar ta na zaman lafiya ne.

Sai dai Kasashen yammacin duniya sun yi imanin cewa Iran na kokarin samar da makaman nukiliya ne.

Karin bayani