An kashe mutane 35 a Iraqi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Galibin hare haren da ake kaiwa sunfi shafar 'yan Shi'a

An kai wasu sababbin jerin hare haren da ake kaiwa da kananan motocin da ke dauke da bama bamai a Iraqi, inda aka hari Bagadaza da kuma birnin Hilla.

Majiyoyina asibiti a Hillan -- birnin da ke a kudu da babban birnin Iraqin sun ce kawo yanzu babban asibitin birnin ya karbi gawarwaki 35 daga hare haren bama bamai, 7 da aka kai da kananan motoci.

Hare hare a babbar Unguwar yan shi'a ta Bagadaza sun yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 14.

A watan bara, mutane fiye da da dubu daya ne aka kashe a munanan hare hare, wadanda galibi suka shafi yan Shi'a da kuma wuraren gwamnati.

Karin bayani