Dabi'ar jima'i don kifi a Kenya

Image caption Yadda ake hada-hada a gabar tekun Victoria

An kiyasta cewa kusan mutane miliyan daya da dubu dari biyar ne ke rayuwa da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV a kasar Kenya.

Matsalar dai ta fi kamari a yankunan karkara, inda masunta suke wani al'amari da aka kwatanta da "ban gishiri in ba ka manda" da matan da suke sayan kifi a wajensu da jima'i maimakon su saya da kudi.

A yanzu haka dai wata kungiyar sa kai a yankin na kokarin sauya wannan dabi'a, ta hanyar karfafawa matan gwiwar mallakar kwale-kwale tare da biyan Masunta kudin kifinsu maimakon tsohuwar dabi'ar musayar kifin da jima'i.

Ana kawo kifayen tun da sanyin safiya a gabar tekun Victoria, kifi irinsu karfasa, ragon ruwa da tarwada.

Da farko mata ne ke saye daga nan su kuma su kai kasuwa don samun karamar riba.

'Jaboya'

Image caption Agnes Auma ta ci gajiyar tallafin da aka bayar

An shafe shekaru mata na biyan masunta kudin kifin da jima'i a wata al'ada da ake kira 'Jaboya'.

Daya daga cikin matan mai suna Lucy Odhiambo ta ce a kwanne mako tana saduwa da maza biyu don su bata kifi.

Odhiambo tace "Ana tilasta mini biyan kudin kifin ta hanyar yin jima'i saboda bani da wata hanya ta biya. Galibi maza biyu ne ke kwanciya dani a kowanne mako. Zan iya samun cuta amma kuma bani da zabi. Mijina ya mutu kuma dole ne in tura 'ya'ya na biyar zuwa makaranta. Na san wannan muguwar dabi'a ce."

Amma kuma abun na raguwa saboda kungiyar Vired mai yaki da sayen kifi da jima'i kuma tuni har mata 19 sun ci gajiyar shirin.

Agnes Auma na daga cikin matan da suka samu tallafi ta ce "Na lura cewa da tuni na mutu idan na ci gaba da baiwa maza jikina saboda kifi. Ba zan iya ci gaba ba. Wannan shirin ya nuna cewar ba zan ci gaba da dogaro da maza ba domin zan iya ciyar da kaina a yanzu".

'Ba zamu daina ba'

Image caption Matan na kokarin ciyar da 'ya'yansu da sana'ar kifi

Wasu masunta sun ce ba za su daina mummunar dabi'ar ba.

Daya daga cikin masunta Felis Ochieng ya ce "Ina kwana da mata uku a kowanne mako kafin na basu kifi kuma na gaji wannan sana'a ce daga wajen mahaifi na. Wasu Matan na sayen rabin kifin da kudi sauran rabin kuma da jima'i. Ina jin kunya, amma sha'awar aika ta haka".

A hankali a hankali ana samu sauki, saboda mata a gabar tekun Victoria sun soma gane hadarin dake tattare da wannan sana'ar.

Sai dai jima'i don kifi abu ne da ke bukatar mutane su canza halinsu don kawo karshen sa.

Sannan kuma ana bukatar karin tallafi daga wajen masu agaji domin 'yanta mayan daga wannan abu.

Karin bayani