Sabon rikici ya barke a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan tawayen sun kai hari garin Malakal mai arzikin mai

Rikici ya barke a Sudan ta Kudu a karon farko tun lokacin da gwamnati da kuma 'yan tawaye suka sanya hannu a kan wata yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Junairu.

'Yan tawayen dake goyan bayan tsohon mataimakin Shugaban Kasar Reik Machar sun kai hari garin Malakal, babban birnin jahar Upper Nile mai arzikin mai.

Dakarun gwamnati sun fafata dasu a wurare daban-daban a garin.

Wakilin majalisar dinkin duniya a Juba, Toby Lanzer ya bukaci dukkanin bangarorin dasu kare fararen hula.

Wannan artabun zai sake rura wutar damuwar da ake da ita game da tsaron filayen hakar man Sudan ta Kudu dake arewacin kasar.

Karin bayani