'Yan Boko Haram sun kai hari a Bama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau da sauran 'yan Boko Haram

Rahotanni daga Bama da ke jihar Borno a Nigeria na cewa wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai farmaki garin da asubahin ranar Laraba.

Sanata mai wakiltar yankin a majalisar dattawan Nigeria, Ahmed Zanna ya shaida wa BBC cewa an kai harin ne da misalin karfe 4:00 na safe.

Mazauna Bama din sun ce harin ya gauraye baki daya sassan garin amma kawo yanzu babu cikakken bayani game da barnar da aka yi daga jami'an tsaron Nigeria.

A baya 'yan Boko Haram sun kai hare-hare a garin Bama, inda aka kashe mutane da dama tare da barnata dukiyar al'umma.

Karin bayani