'Duniya ta yi watsi da al'ummar CAR'

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fararen hula a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya na fargabar rayuwarsu

Kungiyar Likitoci ta Medecins Sans Frontiers (MSF) tayi gargadin cewa tashin hankalin da ake fama da shi a Jamhuriyar Afirka ya kai kololuwa kuma tace akwai bukatar a kara kai kayan agaji.

Kungiyar ta kuma yi zargin cewa Kasashen duniya sun yi watsi da Kasar, sannan kuma tayi kira akan kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya da kuma Kasashen Afirka dasu dau matakin gaggawa domin dakile ta'asar da ake tafkawa a Kasar.

Shugaban Kungiyar Likitocin Dr. Joanne Liu ya shaidawa BBC cewa fararen hula na fargabar rayukansu, kuma ba zasu zauna a asibiti ba tare da kariyar kungiyar ta MSF ba.

Dubun dubatar mutane ne dai suka tsere daga gidajensu.

Karin bayani