'Indiyawa na mutuwa a Qatar'

Ma'aikata a Qatar Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Babu wani cikakken bayanin dalilin mutuwar 'yan ciranin daga Qatar.

Wani rahoto da jaridar Burtaniya ta wallafa ya nuna cewa Indiyawa ma'aikata 'yan cirani fiye da dari biyar ne suka rasa rayukansu a Qatar tun daga shekarar 2012.

Jaridar The Guardian ta ce ofishin jakadancin India da ke Qatar ya tabbatar da adaddin wadanda suka rasun, sai dai dai yi wani cikakken bayanin dalilin mutuwar ta su ba.

Sai dai hukumar kwadagon Qatar ta ce a cikin adadin wadanda suka rasun har da wadanda suka yi mutuwar Allah da Annabi, da wadanda suka mutu sanadiyyar hadarin mota, ko wani tsautsayi a wuraren da suke aiki.

A bangare guda kuma ana ganin yawancin mamatan ma'aikatan da ke aiki tukuru ne don tunkarar wasan kwallon kafa na cin kofin Duniya da Qatar din za ta karbi bakunci a shekarar 2022.

Karin bayani