An kai hari ofishin jakadancin Iran a Labanon

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana danganta hare haren labanon da yakin basasar Syria

Wasu abubuwa masu karfi sun fashe a kudancin kewayen babban birnin Labanon na Beirut inda mutane akalla hudu suka halaka da kuma jikkata wasu.

Wakilin BBC a inda abin ya auku ya ce wasu 'yan kunar bakin wake biyu dake tuka wata mota da kuma wani babur ne suka kaddamar da harin a cibiyar al'adun ofishin jakadancin Iran a lardin Beir Hassan na birnin dake kusa da ofishin jakadancin Kuwait.

Yanki ne dake karkashin kungiyar 'yan shi'a ta Hezbollah.

Wata kungiyar masu yin jihadi ta Abdallah Azzam ta dauki alhakin kaddamar da hare haren.

Ana alakanta yawancin bama baman da suke tashi a baya bayan nan a Beirut da yakin basasar da ake yi a makwabciyar Kasar Syria.

Karin bayani