Sabon salon kai hari a Masar

Prime Ministan Masar Hazem el-Beblawi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A dan tsakanin nan ana yawan kai hari kan masu yawon bude ido 'yan kasashen ketare a yankin Sinai na kasar.

Prime Ministan Masar Hazeem el-Beblawi ya shaidawa gidan talabijin din kasar cewa masu tada kayar baya na yankin Sinai na zama barazana ga masu yawon bude idanu 'yan kasashen ketare.

Hukumomin kasar dai sun ce su na daukar matakan kariya ga masu yawon bude idanun.

Wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba ya nuna cewa, kungiyar masu kaifin kishib islama ta Ansar Bayt al-Maqdis na barazanar kai hare-hare wuraren yawon bude ido da ke kasar Masar a ranar alhamis mai zuwa.

Kuma kungiyar ta dauki alhakin harin kunar bakin waken da aka kai a yankin Sinai a ranar lahadin da ta gabata, wanda ya yi sanadiyar rasa rayukan wasu 'yan asalin kasar Korea su uku.

Wuraren bude idanu na daga cikin abinda ke habaka tattalin arzikin kasar ta Masar, sai dai hakan ya ja baya matuka tun bayan juyin juya halin da kasar ta fuskanta da ya hambarar da gwamnatin shugaba Hosni Mubarak a shekarar dubu biyu da sha daya.

Karin bayani