Saudiyya ta tasa keyar 'yan Somalia 12,000

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akwai dubban 'yanci rani a Saudiyya

Hukumomi a Saudi Arabia sun tasa keyar 'yan kasar Somalia kusan 12,000 tun daga farkon wannan shekarar, ciki hadda mata da kananan yara.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce an tasa keyar mutanen ba tare da basu damar kasancewa 'yan gudun hijira ba.

Kungiyar ta bukaci hukumomin Saudiyya su kawo karshen korar baki daga cikin kasarsu saboda ya sabawa dokokin kasa da kasa da kuma 'yancin rayuwar jama'a.

'Yan Somalia bakwai da kungiyar ta tattauna dasu a Mogadishu sun ce gwamnatin Saudiyya ta tsare su na tsawo makwanni a kurkuku cikin mawuyacin hali.

A cewarsu, an kuma hanasu ganawa da jami'an hukumar 'yan gudun hijira da Majalisar Dinkin Duniya kafin a tasa keyar tasu.

Karin bayani