'Inganta rayuwar 'yan Indonesia a Saudiya'

'Yan cirani a Indonesia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin cewa ana cin zarafin ma'aikatan Indonesia a Saudiya

Saudi Arabiya ta sanya hannu kan wata yarjejeniya tare da Indonesia da nufin kare hakkokin masu aikin boyi boyi 'yan asalin Indonesia a cikin Kasar.

Sanya hannu kan yarjejeniyar ya biyo bayan zarge zargen cewa ana cin zarafin ma'aikatan.

Yarjejeniyar tace daga yanzu ba za a sake kwace musu fasfo din su ba.

Ba za kuma a hana su yin magana da 'yan uwansu ba, a lokacin da suke aiki.

Za kuma a basu tabbacin biyansu hakkinsu, sannan za a ware masu ranakun da zasu rika hutu.

Indonesia dai ta shafe shekaru 4 tana matsawa don ganin an kyautata rayuwar 'yan kasar ta, dake Saudiyya.

Hakan kuwa ya biyo bayan zarge zargen yin lalata da ma'aikatan da kuma rashin biyansu hakkokinsu.

Karin bayani