Rikici ya rincabe a Ukraine

Hakkin mallakar hoto ukraine
Image caption An tura karin dakarun gwamnati a Kiev

Ma'aikatar tsaro ta Ukraine ta tabbatar da cewar za ta aike da sojin kundunbala zuwa Kiev babban birnin kasar.

Ta jaddada cewar rawar da za su taka za ta kasance ta kare ofisoshin gwamnati da kuma cibiyoyin soji,amma ba don tinkarar masu zanga zangar kin jinin gwamnati ba.

Tashin hankalin ya yadu zuwa sauran garuruwa da birane; an kai wa Hedikwatar 'yan sanda hari a birnin Lviv na yammacin kasar da kuma gine ginen gwamnati a Ternopil.

Kasashen duniya sun soma mayar da martani mai kwari game da abubuwan da ke faruwa a Ukraine.

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bukaci shugabannin 'yan adawa su dakatar da zubar da ini, su kuma gaggauta komawa kan sansantawa tare da gwamnati.

Ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai za su gudanar da wani taro na musamman a ranar Alhamis yayinda ake sa ran za a sa ka wasu matakan takaici a kan wadanda keda alhakin tashin hankalin.

Karin bayani