An kashe mutane 13 a Barkin Ladi

Image caption Jihar Filato na tsakiyar Nigeria

'Yan bindiga sun kashe mutane 13 ciki hadda yara tara a kauyen Rapyem dake karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filaton Nigeria.

Rahotanni sun nuna cewar an kai harin ne a cikin daren ranar Laraba.

Kawo yanzu ba a san wadanda suka kai harin a kan 'yan kabilar Berom ba.

Ana zaman doya da manja tsakanin kabilar Berom da ta fulani a jihar filato lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama.

Karin bayani