Godwin Emefiele zai maye gurbin Sanusi

Hakkin mallakar hoto cbn facebook page
Image caption Shalkwatar babban bankin Nigeria

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya aike wa majalisar datijjan kasar sunan Manajan Darektan bankin Zenith, Mr Godwin Emefiele don maye gurbin Sanusi Lamido Sanusi a matsayin gwamnan babban bankin Nigeria.

Jim kadan bayan dakatar da Malam Sanusi ne, Mr Jonathan ya mika sunan Mr Emefiele.

Dan majalisar dattijai, Sanata Ahmed Lawan ya tabbatar wa BBC cewar sun samu wasikar shugaban kasar kan sabon mutumin da ya keson ya zama gwamnan babban bankin kasar.

Ita kuwa majalisar wakilan kasar, ta yi Allawadai ne da matakin dakatar da Malam Sanusi Lamido Sanusi a matsayin gwamnan babban bankin kasar.

Wasu 'yan majalisar wakilan na kallon matakin Shugaba Jonathan a matsayin nuna alamun rashin gaskiya a cikin gwamnatinsa.

Karin bayani