Facebook ya sayi WhatsApp

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Facebook da Whatsapp sun kulla yarjejeniya a ranar Laraba

Shafin Facebook ya sayi manhajar WhatsApp a kan tsabar kudi $19bn da kuma ta hanyar sayen hannun jarin sa.

Wannan shine ciniki mafi girma da Facebook ya yi ya zuwa yanzu.

Mutane sama da miliyan 450 ne ke amfani da manhajar WhatsApp.

Manhajar nada farin jini ga mutanen da suke son kaucewa cajin kudi wajen tura rubutaccen sako.

A wata sanarwar kulla yarjejeniyar da aka fitar, mutumin da ya kirkiro Facebook Mark Zuckerberg ya bayyana abubuwan da manhajar WhatsApp ke samarwa a matsayin 'masu matukar amfani'.

WhatsApp na baiwa masu amfani da manhajar damar aikewa da sakonni ta hanyar kaucewa cajin rubutattun sakonnin da aka aika.

Kamfanin ya yi ikirarin cewa a yanzu haka yana yi wa masu amfani da manhajar su miliyan daya a rana rajista.

'Sabbin attajiran Silicon Valley'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban Facebook, Mark Zuckerberg

Wannan yarjejeniyar cinikin ta kunshi tsabar kudi $4bn da kuma tsabar kudi kusan $12bn na hannayen jarin Facebook da kuma karin $3bn na kaya ga wadanda suka kirkiri WhatsApp da kuma ma'aikatansa daga baya.

A wani taro da aka kira domin tattauna wannan yarjejeniyar, daya daga cikin mutanen da suka kirkiri WhatsApp Jan Koum ya ce yana shirin gudanar da kamfanin ba tare da hada kai da wasu ba.

Zai kuma kasance mamba a kwamitin daraktocin Facebook.

"Mun yi farin ciki da kulla hulda tare da Mark da kuma Facebook, yayinda zamu ci gaba da tallatawa mutane abinda muka samar a fadin duniya", in ji Mr Koum.

Mutumin da ya kirkiro Facebook ya ce ya yi imanin cewa manhajar WhatsApp na kan hanyar samun mutane biliyan daya na masu amfani da manhajar, amma ya jaddada cewa ba shi da shirin sanya talla akan manhajar WhatsApp .

'Awon-gaba da biliyoyi'

Cathy Boyle, wata mai sharhi ce a wani kamfanin yin bincike na eMarketer, kuma ta ce bayan harkar tallace- tallace manhajar WhatsApp nada amfani sosai ga Facebook saboda dalilai da dama , wanda suka hada da farinjinin da yake da shi a kasashen ketare.

Ms Boyle ta fadawa BBC cewa "WhatsApp ya samu damar shiga cikin harkokin kasuwannin duniya sosai fiye da Facebook".

Ta kara da cewa an fahimci cewa babban jami'in hadar- hadar kudaden kamfanin Facebook David Ebersman ya yi la'akari ga kamfanonin sadarwa a lokacin da ake tattauna sayen manhajar WhatsApp.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Facebook na da miliyoyin mutane da suka yi rijista da shi.

Jami'ar ta ce " Manhajar WhatsApp na kokarin awon-gaba ne da biliyoyin da kamfanonin sadarwa zasu samu".

Hannayen jarin a Facebook sun fadi da kashi 5% kafin su dan yunkuro daga baya.

Kafin wannan ciniki dai, Facebook ya sayi manhajar Instagram a kan $1bn a shekarar 2012.

An kuma bada rahotan cewa Facebook ya yi tayin sayen manhajar Snapchat wacce ake aika sakon hoto ta hanyar ta akan kudi $3bn.

Karin bayani