Tukwici kan 'yan Al-Qaida a Iraki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akwai dubban mayakan sa-kai a Iraki

Gwamnatin Iraki ta yi tayin bada ladar dala dubu 17 a kan kowane mai fafutuka guda dake da alaka da kungiyar al Qaida da za a kashe.

An bada sanarwar ce a shafin Inatanat na ma'aikatar tsaron kasar.

Haka zalika, ma'aikatar ta yi tayin bada irin wannan lada ga duk wanda zai taimaka a kama masu fafutika na kungiyar nan ta Daular Musulunci ta Iraki da Sham.

Kungiyar dai tana da hannu a hare-haren kunar bakin wake da dama da aka kai a Irakin a 'yan shekarun nan, abun da ya sa aka samu karuwar tashin hankalin da baa taba ganin irinsa a kasar ba tun shekara ta 2008.

Karin bayani