Matsalar zazzabin cizon sauro a duniya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mutane na mutuwa sakamakon cizon sauro a duniya.

Wata kungiyar Likitoci a duniya ta bayyana cewar ana samun nasara wajen yaki da cutar zazzabin cizon sauro (malaria) a nahiyar Afrika, amma kuma bai kamata a dakatar da azamar kawar da cutar ba.

Likitocin a wani rahoto a mujallar Lancet, sun ce har yanzu akwai mutane miliyan 184 wadanda rabinsu yara ne kananan na zama a wuraren dake da alamun za su iya kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro ko kuma maleriya.

Sun ce akwai jan aiki a gaban hukumomi don kawar da hadduran da ake dasu a wasu wuraren.

Mutane 627,000 ne ke mutuwa a duniya a duk shekara sakamakon cutar maleriya wadanda galibinsu a Afrika suke.

Rahoton ya ce duk da yawan kudaden da ake kashewa domin yaki da cutar zazzabin cizon sauro, kawo yanzu kusan kashi hamsin da bakwai cikin dari na al'ummar nahiyar Afrika na fuskantar barazanar kamuwa da cutar.

Marubuta rahoton sun ce akwai bukatar a kara yawan gidan sauro mai magani a kasashen da cutar zabbabin cizon sauro ke addabarsu.

Karin bayani