Zan kai Jonathan kotu—Sanusi

Image caption Malam Sanusi ya ce zai kalubalanci dakatar da shi.

Gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi wanda aka sanar da dakatar da shi ya bayyana cewa zai kalubalanci dakatarwar da aka yi masa a kotu.

Malam Sanusi Lamido ya ce ba zai bari wannan lamari ya wuce ba saboda gaba.

A ranar Alhamis ne Shugaba Goodluck Jonathan ya dakatar da gwamnan babban bankin nan take daga mukaminsa a cikin wata sanarwa daga fadar shugaban kasar.

Tsohon gwamnan babban bankin ya ce zai kalubalanci shugaban kasar ne, ba don yanason koma wa kan kujerar sa ba, a a saboda kare cin gashin kan babban bankin

Ya kuma shaidawa BBC tun a watan Oktobar bara ya yi niyyar barin kujerar sa amma saboda manya sun bashi shawarar ya ci gaba da rike mukamin har zuwa karshen wa'adinsa.

Ya kuma kalubalanci rashin aike masa da abubuwan da ake tuhumar sa da aikatawa a rubuce.

Hakkin mallakar hoto cbn facebook page
Image caption Shalkwatar babban bankin Nigeria a Abuja

Malam Sanusi lamido ya ce dukkanin irin zarge-zargen da ya fito da su a majalisa, ba ra'ayin kansa bane, amma matsayi ne na babban bankin kasar.

'Sabon gwamna'

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya aike wa majalisar datijjan kasar sunan Manajan Darektan bankin Zenith, Mr Godwin Emefiele don maye gurbin Sanusi Lamido Sanusi a matsayin gwamnan babban bankin Nigeria.

Jim kadan bayan dakatar da Malam Sanusi ne, Mr Jonathan ya mika sunan Mr Emefiele.

Ita kuwa majalisar wakilan kasar, ta yi Allawadai ne da matakin dakatar da Malam Sanusi Lamido Sanusi a matsayin gwamnan babban bankin kasar.

Tuni darajar kudin Nigeria ta fadi kasa warwas sannan sakamakon dakatarwar.

Masana kan harkokin tattalin arziki sun ce darajar naira ta fadi idan aka kwantanta da dalar Amurka.

Karin bayani