Jonathan ya dakatar da Sanusi Lamido

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An dakatar da Sanusi lamido

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya dakatar da gwamnan babban bankin kasar, Malam Sanusi Lamido Sanusi nan take daga mukaminsa.

Wata sanarwa data fito daga fadar shugaban Nigeria ta ce gwamnati tayi la'akari ne da rahotan hada-hadar kudade na Nigeria da kuma wasu kungiyoyi wanda ya nuna karara cewa zamanin mulkin Malam Sanusi na cike da sakaci da kudade da kuma rashin da'a, wanda kuma yaci karo da manufar babban bankin na Nigeria.

Sanarwar ta ce domin ganin an sake dawo da martabar babban bankin Nigeriar da kuma mutunta doka da kuma oda da gaskiya da amana shi ne yasa shugaba Jonathan ya dauki matakin.

Shugaban Jonathan a cewar sanarwar ya bada umanin cewa Mallam Sanusi ya mika ragamar shugabancin babban bankin zuwa mataimakiyar gwamnan babban bankin mafi girman mukami, Dr. Sarah Alade wacce za ta rike mukamin na rikon kwarya har sai an kammala bincike.

Image caption Wasu na ganin matakin Shugaba Jonathan zai shafi tattalin arzikin kasar.

Shugaban Kasar ya ce yana fatan Dr. Alade za ta maida hankali wajen ci gaban bankin da kuma dawo da kimar babban bankin a idon kasashen duniya.

Daga karshe sanarwar fadar shugaban kasar ta sake tabbatarwa da dukkanin masu ruwa da tsaki a bangaren hadar-hadar kudaden kasar cewa an dauki mataki ne da kyakyawar manufa da kuma don ci gaban tattalin arzikin Nigeria tare kuma da bin doka da kuma oda.

'Takun saka'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministar kudin Nigeria, Ngozi Okonjo Iweala

A cikin 'yan watannin na ana zaman doya da manja tsakanin Sanusi Lamido Sanusi da fadar shugaban Nigeria, saboda zargin da gwamnan babban bankin ya yi cewar kamfanin man kasar NNPC da kin yin bayani game da $49.8 biliyan na kudaden danyen mai.

Bayan da Sanusi Lamido ya yi wannan zargin a wata wasika ga shugaban kasar, sai galibin kafofin yada labaran kasar su ka samu bayannan dake cikin wasikar, abinda kuma bai yiwa fadar shugaban kasar dadi ba.

A cikin watan Junairu, Mr Jonathan ya bukaci Sanusi Lamido ya yi murabus, amma sai gwamnann babban bankin ya ce bai zai yi murabus ba, har sai wa'adin mulkinsa ya kare.

Daga bisani wasu dattawa a kasar sun sasanta rashin fahimtar junar da ta kunno kai tsakanin Shugaban kasa, da kuma gwamnan babban bankin saboda a cewarsu, rashin jituwar na iya tasiri a kan tattalin arzikin kasar.

Karin bayani