An fara shari'ar 'yan Al-Jazeera a Masar

Masu zanga-zangar bukatar a saki ma'aikatan Al-Jazeera Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An dai gudanar da zanga-zanga a kasar ta Masar, tare da bukatar hukumomin kasar da su saki ma'aikatan Al-Jazeera da suke tsare da su.

A yau ake shari'ar 'yan jaridar Al-Jazeera nan gudu uku a Birnin Alkhahira, a wata shari'a da ta ja hankalin kasashen duniya wadda ake gani zakaran gwajin dafi ne game da batun 'yancin fadar albarkacin baki a kasar Masar.

Ana dai tuhumar 'yan Jaridar da laifin yada labaran da ba na gaskiya ba, da kuma taimakawa kungiyar 'yan uwa musulmi.

An kama su tun a watan Disambar shekarar da ta gaba,kwanaki kadan bayan da hukumomin kasar da Sojoji ke marawa baya sun ayyana Kungiyar 'yan uwa musulmi da ta 'yan ta'adda.

Al-jazeera dai ta bayyana zarge-zargen da ake musu da cewa ba shi da tushe bare makama, daya daga cikin wadanda ake tuhumar tsohon ma'aikacin BBC ne mai suna Peter Gresta.