Jirgin sojin Libya ya tarwatse a Tunisia

Jirgin Libya
Image caption Jirgin na dauke ne da marasa lafiya biyar 'yan Libya

Wani jirgin saman sojin Libya da ake amfani da shi wajen daukar marasa lafiya ya tarwatse a kudu maso gabashin babban birnin Tunisia kuma dukkanin ma'aikatan jirgin su 11 sun mutu tare da pasinjojin dake ciki.

Jirgin na dauke ne da marasa lafiya biyar 'yan Libya.

Za a kai marasa lafiyar wani asibitin Tunisia ne domin a basu magani.

Jirgin dai ya fado ne a wata gona mil 15 daga filin jirgin saman Tunis

Karin bayani