Ana bukatar karin dakaru a CAR

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kiritoci na ci gaba da kashe Musulmi a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

Sakatare Janar na majalisar dinkin duniya, Ban Ki-moon ya ce ana bukatar karin 'yan sanda da sojoji 3,000 a jamhuriyar dimokradiyyar Congo domin kare fararen hula daga rikicin da ake fama da shi.

Tuni dai aka girke dubunnan dakarun kasashen Afrika da na Faransa a kokarin dakile fadan da ake yi tsakanin 'yan tawayen Seleka wadanda yawancinsu Musulmi ne da kungiyar mayaka masu tsananin kishin addinin Kirista ta Anti-Balaka.

Wakilin BBC a majalisar dinkin duniya ya ce da alama sai majalisar ta kai dakarunta na kiyaye zamna lafiya kasr, amma za a dauki watanni kafin kai wa ga hakan, duk da cewa ana bukatar karin dakarun nan take domin kwantar da rikicin.

Karin bayani