Ana ci gaba tsokaci kan dakatar da Sanusi

Image caption Wasu na ganin cewar akwai siyasa a cikin dakatar da Sanusi

Ana ci gaba da tsokaci game da dakatawar da aka yi wa gwamnan babban bankin Nigeria, Sanusi Lamido Sanusi.

Kungiyar Arewa Elders Forum ta bukaci gwamnatin tarayyar kasar da ta bada wasu gamsassun bayanai na dalilan da suka sa ta dakatar da gwamnan.

A ganin kungiyar dai gwamnatin kasar ba ta bi ka'idojin da suka dace wajen dakatar da gwamnan bankin ba, saboda haka ta bukace shi da ya garzaya kotu, tana mai cewar dakatar da shi din bita da kulli ne kawai.

Babbar jam'iyyar adawa ta Nigeria, APC ta ce matakin ya saba dokar da ta ce majalisar dattawa ce kadai za ta iya sauke gwamnan babban bankin kasar.

Gwamnatin Nigeria ta bayyana dalilan da ta ke zargin gwamnan babban bankin kasar da aikatawa, wadanda a cewarta suka sa ta dauki matakin dakatar da shi daga mukaminsa.

Sanarwar wadda ke dauke da sa hannun sakataren gwamnatin tarayya, Anyim Pius Anyim, ta zayyana jerin abubuwan da ta ce laiffuka ne da ta ke zarginsa ciki hadda batun "kashe kudi ba bisa ka'ida ba, da kuma sabawa ka'idojin aiki".

Karin bayani