An yi jana'izar Komla Dumor

An yi jana'izar jana'izar ma'aikacin BBC nan Komla Dumor dazu a Accra babban birnin kasar sa ta haihuwa, Ghana.

Komla mai shekaru 41 ya rasu ne a London a watan jiya.

Cikin wadanda suka halarci jana'izar harda shugaban kasar, John Mahama.

An ajjiye gawarsa a cocin Holy Spirit Cathedral a birnin Accra inda mutane suka nuna alhihini su.

Karin bayani