An kama kasurgumin me hada-hadar kwayoyi

Joaqim Guzman Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Joaqim Guzman wanda aka kama a Mexico

An kama daya daga cikin manyan gawurtattun masu hada-hadar miyagun kwayoyi da ake nema ruwa a jallo a duniya a Mexico.

An gabatar wa manema labarai Joaquin Guzman wanda ake wa lakabi da El Chapo ko Shorty, a wani sansanin soji a birnin Mexico.

Tun a shekara ta 2001 ake neman sa lokacin da ya tsere daga wani gidan yari me tsaron gaske, ta cikin kwandan kayan wanki.

Shugaba Enrique Pena Nieto ya ce an damke Shorty Guzman ne a wurin shakatawa na bakin teku na Mazatlan, da ke jiharsa ta Sinaloa.

An samu nasarar kama tsohon shugaban kungiyar ta Sinaloa da taimakon jami'an yaki da miyagun kwayoyi na Amurka.

Kungiyar hada hadar miyagn kwayoyin ta Sinaloa tana satar shigar da hodar iblis ta cocaine da ganyen wiwi da kuma sauran nau'in miyagun kwayoyi zuwa cikin Amurka.