Shugaban Ukraine ya gudu daga Kiev

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Viktor Yanukovych ya ce ba zai sauka daga mulki ba

Shugaban kasar Ukraine Viktor Yanukovich ya tsere daga babban birnin kasar Kiev, inda ake zaton yana yankin gabashin kasar byan matsin lamba kan ya yi murabus.

Shugaban ya kafe duk da kuri'ar da 'yan majalisar dokoki suka kada da farko ta tsige shi daga mulki cewa ba zai yi murabus ba.

Da ya ke jawabi ta wani gidan talabijin a birnin Kharkiv, Mr Yanukovich, ya bayyana abubuwan da aka yi ta yi mishi na adawa da cewa juyin mulki ne.

Gwamnonin yankunan gabashin kasar sun gana a Kharkiv, da manyan jami'an gwamnatin Rasha domin tattauna abinda suke gani na rashin halarcin wadanda ke rike da babban birnin kasar Kiev.

Wakilin BBC a Kharkiv, ya ce hakan na sa tsammnin karin rarrabuwar kai da rikici a kasar ta Ukraine.

Karin bayani