Jakadan Rasha a Ukraine ya koma gida

Oleksandr Turchinov, Shugaban rikon Ukraine Hakkin mallakar hoto b
Image caption Oleksandr Turchinov, Shugaban rikon Ukraine

Rasha ta kirawo jakadanta na Ukraine gida, domin ganawa da shi a kan abin da ta bayyana da tabarbarewar yanayi a Kiev.

Rashan ta yi hakan ne bayan da sabon shugaban rikon kwaryar da aka nada na Ukraine, Oleksandr Turchinov ya bayyana cewa , babban abin mai da hankali akai yanzu shi ne komawa ga turbar hadin kan Turai

Mr Turchinov, ya ce, a shirye yake ya tattuna da Rasha,in har ta mutunta abin da ya kira zabin da Ukraine ta yi na hulda da Turai.

Sai dai kuma har wa yau , ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya zargi Ukraine da saba yarjejeniyar da aka kulla ranar Juma'a.

Kungiyar gamayyar Turai kuwa ta ce babbar jami'arta ta harkokin kasashen waje, Catherine Ashton, za ta je Kiev yau Litinin domin nuna goyon baya ga sabon shugabancin kasar ta Ukraine.

Karin bayani