Majalisar Ukraine ta ce a tsige Yanukovych

'Yan majalisar dokokin Ukraine

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

'Yan majalisar dokokin Ukraine

Majalisar dokokin Ukraine ta kada kuri'ar neman sauke shugaban kasar, Viktor Yanukovych, daga kan mulki.

A lokacin da aka sanar da sakamakon kuri'ar da majalisar ta kada, zauren majalisar ya rude da gude-gude da shewa, kuma zababbun sun bige da raira taken kasar.

Wata mai magana da yawun shugaban ta ce matakin ya saba wa doka.

'Yan majalisar sun kuma tsayar da ranar 25 ga watan Mayu a matsayin lokacin da zaa gudanar da zaben shugaban kasa, kafin cikar wa'adin mulkin Yanukovych.

Sai dai tun farko Shugaban Ukraine din ya ce sam-sam ba zai yi murabus daga mukaminsa ba.

Ya kuma bayyana matakan da masu adawa da shi a majalisar dokokin su ka dauka da cewa, halayya ce ta 'yan banga, kuma juyin mulki ne.

Ya ce, majalisar din ta keta doka bayan da ta zabi sabon kakaki, sannan kuma ta bada umurnin a saki jagorar 'yan adawa, Yulia Tymoshenko, daga gidan kurkuku nan take.

A yanzu an saki Yulia Tymoshenkon kuma tuni ta isa Kiev babban birnin kasar, domin ganawa da masu zanga zanga a dandalin 'yancin kai.

Rahotanni daga Ukraine din sun ce, shugaba Viktor Yanukovych, yayi kokarin tserewa zuwa Rasha amma aka hana jirginsa tashi.